Faransa ta ce za ta yi iyakacin kokarin ta na ganin ta kubutar da 'yan kasar bakwai da aka sace a kasar Kamaru ana yin garkuwa da su
Karshen ta dai Chuck Hagel ya zama sakataren tsaron Amurka duk da kokarin da wasu 'yan Republican su ka yi na neman hana tabbatar da shi
Wani jirgin ‘yan yawo bude ido mai siffar balom-balo yayi hadari kusa da birnin Luxor a Masar, kuma ya kashe ‘yan yawon bude ido su 19 da suke ciki.
Faransa tace ba zata yi shawarwari da mutanen da suka kama wasu ‘yan kasarta cikin makon jiya a Kamaru suna garkuwa da su ba.
Jami’ai manyan kasashen dunya shida da Iran suna shawarwari dangane da shirin nukiliuyar kasar da ke janyo gardama, a mataki na baya-bayan nan da nufin warware damuwa da ake da shi fiye da shekaru 10 cewa Iran tana kokarin kera makamin nukiliya.
Sabon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai fara ziyarar aikinsa ta farko zuwa kasashen ketare, tun bayanda ya karbi aiki daga hanun Hillary.