Labarai

An Kori Karin Ma'aikata Dubu UKu Da Dari Shidda A Afrika Ta KuduKimanin ma’aikatan hakar mu’adinai dubu uku da dari shida aka kora jiya Talata yayinda kungiyar kwadago take ci gaba da tada kayar baya a kamfanonin hakar mu’addanan kasar. Kamfanin hakar mu’adanai na Atlatsa Resources yace ya salami ma’aikata dubu biyu da dari daya da sittin, wadanda suka shiga  yakin aiki tun ranar daya ga wannan wata na Oktoba,  a kamfanin karafanta na Bokoni. Kamfanin ya bayyana cewa, ma’aikatan suna da zuwa karshen wunin yau Laraba su daukaka kara. Tun farko ...