Maras Hoto
Search

arewacin Nigeria

03/11/2008

A arewacin Nigeria inda Musulmai suka fi runjaye ana samun karuwar al'umar yankun karkara da suke yin amfani da dabarun bayar da tazarar haihuwa na zamani da kuma sunadarai. Mata a kauyen Zakire dake cikin jihar Kano, sun rungumi shirin bayar da tazararar haihuwa domin suna yin tururuwa zuwa asibitin Zakire don su amfana da shirin saboda fa'idarsa ga lafiyar iyali masnman mata da yara.

 

Wata mace 'yar shekra 32 da haihuwa mai suna Rabi'atu Musa, ta sheda wa wakilnmu cewa, ta na da yara bakwai. Ta ce da taimakon kungiyar hadaka wato Community Coalition a turance, masu wayar da kan magidanta, mijinta, wanda manomi ne, ya amince ta zo asibitin don ta amfana da shirin bayar da tazarar haihuwa don ta samu hutun.Women with children wait for care at village clinic in Chad

 

Hauwa Umar, ma'aikaciyar jinye wato Nas a sashen bayar da tazararar haihuwa, ta bayyana cewa, a da, sun fara shirin da mata goma (10) a sati, yanzu suna yin aiki daga litinin zuwa juma'a, kuma a kullun suna samun mata kimanin ashirin (20) masu zuwa don bayar da tazararar haihuwa. Ta ce ma'aikatan jinya suna da muhimmiyar rawar takawa don dorewar sauyin fahimtar da al'umar yankin da suka samu.

 

Kungiyar COMPASS mai samun tallafi daga hukumar raya kasashe ta Amurka, wato USAID, wacce ta fara aiki a shekara ta 2004, ta taka rawar gani wajan kara inganta lafiya da ilimin mata a jihohin arewa biyu da kuma biyu a kudancin Nigera.

 

Mohammed Gama, jamin wayar da kan jama'a ne a COMPASS. Ya kuma bayyana wa cewa, sun baiwa kowa damar bayar da tasa guummuwar wajan shawo kan al'umar yankin Zakire su rungumi shirin bayar da tazarar haihuwa, koda mutun baya da ilimi. Wannan basirar da suka yi amfani da ita, ya nuna zahirin irin nasarar da kungiyar Compass ta samu wajan wayar da kan al'uma masu ra'ayin rikau su fahimci sahihiyar hanya ta kula da lafiyar iyalansu.

 

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Hamas Tayi Watsi Da Wasu Sharuddan Tsagaita Wuta

  Karin Labarai
Isra'ila Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Cibiyoyin Hamas A Rana Ta 16 A Jere
Litinin Kotun Daukaka Kara Ta Afirka Ta Kudu Zata Yanke Hukumci Kan Shari'ar Jacob Zuma
Mawakan Kungiyar Firqatul Sahwa Sun Yi Mummunan Hatsarin Mota  Audio Clip Available
Masana Sun Ce Ana Iya Rigakafin Sulusin Dukkan Cutar Sankara
Kasar Sin Ta yi Gargadi Game Da Cutar Murar Tsuntsaye...
Hukumomin Jihar Kano Sun Jefa Alhaji Hamisu Lamido Iyantama A Kurkuku  Audio Clip Available