Maras Hoto
Search

 
kotun kasar Chad ta fara yin tambayoyi akan turawan nan goma da suka rage daga cikin wadanda aka cafke da laifin yunkurin satar yara

06/11/2007

Wata kotun kasar Chad ta fara yin tambayoyi akan turawan nan 10 da suka rage daga cikin wadanda aka cafke da laifin yunkurin satar yara 103 da ficewa da su daga kasar ta Chad ta jirgin sama. Tun jiya aka faraway yi wadanan turawan da suka hada da ‘yan kungiyar hankoron bada agajin nan ta Zoe’s Ark da kuma ukku daga cikin matuka jirgin da aka so anfani da shi wajen ficewa da yaran.

A yanzu kuma, babbar jigon aiyukkan bada agaji ta MDD dake Sudan ta shiga sahun masu fada aji da suka fito suna Allah-waddai da wannan yunkurin da aka yi na fitar da wadanan yaran daga Chad. A cikin sanarwar da ta bada jiya Litinin ne, Ameerah Haq take cewa ba za’a taba yarda da duk wani yunkuri na raba yara da iyayensu da kuma cire su daga gidajensu da niyyar a fita da su zuwa wata kasar waje ba tareda an bi ka’idodjin da aka shimfida ba.
Chadian President Idriss Deby, center, as he visits children being held in an orphanage in Abeche, Chad
Chadian President Idriss Deby, center, as he visits children being held in an orphanage in Abeche, Chad

Malama Ameerah tace MDD na taimakawa wajen neman sanin yaran da abin ya shafa ta yadda za’a san yadda za’a maida su wajen iyayensu. A can birnin Paris na Faransa kuma, daya daga cikin ‘yanjaridun Faransa da aka sako daga cikin wadanda aka Kaman, yace ‘yan cibiyar bada agajin na Zoe’s Ark sun nuna su wawaye ne kuma sun shata musu karya gameda shirinsu na sace wadanan yaran da fita da su daga Chad.

March Garmirian yace akwa8i wani lokacin da ‘yan wannan cibiyar suka rinka daura wa yaran bandeji, har da saka musiu aydin, don aga kamar suna da alamar jin rauni.

emailme.gif Aika da Wannan sako ta E-Mail
printerfriendly.gif Buga Wannan Shafin

  Muhimmin Labari
Hamas Tayi Watsi Da Wasu Sharuddan Tsagaita Wuta

  Karin Labarai
Isra'ila Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Cibiyoyin Hamas A Rana Ta 16 A Jere
Litinin Kotun Daukaka Kara Ta Afirka Ta Kudu Zata Yanke Hukumci Kan Shari'ar Jacob Zuma
Mawakan Kungiyar Firqatul Sahwa Sun Yi Mummunan Hatsarin Mota  Audio Clip Available
Masana Sun Ce Ana Iya Rigakafin Sulusin Dukkan Cutar Sankara
Kasar Sin Ta yi Gargadi Game Da Cutar Murar Tsuntsaye...
Hukumomin Jihar Kano Sun Jefa Alhaji Hamisu Lamido Iyantama A Kurkuku  Audio Clip Available