VOANews.com

 

Yau A VOA:

Labarai Cikin Harsuna 45
Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Mai Yuwa A Sami Karin Koma  Bayan Tattalin Arziki A Duniya Badi.

02/12/2008

Global Markets ReactKasuwannin hannayen jarin ƙasashen turai sun cira yau yayinda na ƙasashen Asiya da Amurka ke ci gaba da faɗuwa.Kasuwannin hanayen jari na ƙasashen Asiya sun faɗi ainun sakamakon bayanin MƊD da ya nuna cewa ya yiwu a fuskanci koma bayan tattalin arziki mai tsanani a ƙasashen duniya shekara mai zuwa. 

Farashin ɗanyan mai ya yi irin faɗuwar da bai taɓa yi ba cikin shekaru uku a birnin New York bisa la’akari da rage bukatar man da masu zuba jari ta wannan fannin suke yi. Babban ma’aunin hanayen jari na Nikkei a ƙasar Tokyo ya yi ƙasa da kimanin kashi 6% yayinda Hang Seng ya yi ƙasa da kashi 5%. Hanayen jarin ƙasashen turai sun faɗi da sama da kashi 1% sai dai kafin faɗuwar rana sun cira da sama da kashi 1%.

Babban bankin ƙasar Australia ya rage kuɗin ruwa da kashi 1% yau da nufin jawo ra’ayin abokan kasuwanci. Wannan ne rage kuɗin ruwa na huɗu da aka yi a ƙasar cikin watanni huɗu. Ƙarfin arzikin ƙasar Australia ya sa ƙasar bata fuskanci koma bayan tattalin arzikin da ƙasashen amurka da Turai da kuma Japan ke fuskanta sai dai ya daina bunƙasa a cikin ’yan watannin nan.


E-mail This Article Aika Labarin Nan ma Wani Ta E-Mail
Print This Article Shafi Mai Saukin Bugawa
  Muhimmin Labari
Hamas Tayi Watsi Da Wasu Sharuddan Tsagaita Wuta

  Karin Labarai
Isra'ila Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Cibiyoyin Hamas A Rana Ta 16 A Jere
Litinin Kotun Daukaka Kara Ta Afirka Ta Kudu Zata Yanke Hukumci Kan Shari'ar Jacob Zuma
Mawakan Kungiyar Firqatul Sahwa Sun Yi Mummunan Hatsarin Mota  Audio Clip Available
Masana Sun Ce Ana Iya Rigakafin Sulusin Dukkan Cutar Sankara
Kasar Sin Ta yi Gargadi Game Da Cutar Murar Tsuntsaye...
Hukumomin Jihar Kano Sun Jefa Alhaji Hamisu Lamido Iyantama A Kurkuku  Audio Clip Available