VOANews.com

Muryar Amurka ▪ Hausa Majiya Kwakkwara

16 Janairu 2009 

Yau A VOA:

Labarai Cikin Harsuna 45
  Shirye-Shiryenmu


Bayanin Shirye-shiryen Sashen Hausa
(Dukkan lokuta, agogon UTC ne)

LAHADI

0500-0530: Amsoshin Tambayoyinku

Filin dake amsa kowace tambayar mai sauraro kan kowane irin batu, kama daga yadda aka fara kirkiro tauraron dan Adam zuwa ga mutumin da ya fi kowa tsawo a duniya, ko kasar da ta fi zafi ko sanyi a duniya.

1500-1530: Hira Da Baki

Wannan fili yana tattaunawa da bakin da suka kawo ziyara Amurka daga kasashenmu na Afirka domin jin abubuwan dake tafe da su da kuma yadda suka ga abubuwa a bakuwar kasa.

1500-1530: Sakonmu Na Mako

Wane muhimmin batu ne Amurka da Amurkawa suke fuskanta cikin wannan mako? Ina musabbabinsa, kuma ina aka dosa? Wannan fili shi ke fede biri har wutsiya dangane da wannan.

1500-1530: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

LITININ

0500-0530: Rahotannin Bayan Labaru

0500-0530: Noma Tushen Arziki

A cikin wannan filin ana nazarin sabbin dabarun noma na zamani wadanda zasu iya taimakawa manomanmu wajen inganta nomansu da irin amfanin da suke samu.

1500-1530: Rahotannin Bayan Labaru

1500-1530: Ilmi Garkuwar Dan Adam


Wannan fili yana nazarin tsare-tsaren ilmi a kasashen duniya, musamman kasashenmu na Afirka, da irin ci gaban da ake samu a fanning koyarwa da karatu.

1500-1530: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

2030-2100: Rahotannin Bayan Labaru, Rahotanni Kan Harkokin Taimakawa Kai, Ra'ayin Gwamnatin Amurka

TALATA

0500-0530: Rahotannin Bayan Labaru

0500-0530:   Gani Ya Kori Ji...


A cikin wannan shirin, ana tattaunawa da mutanen da suka yiwo kaura zuwa nan Amurka daga wasu kasashe irin namu, domin su bayyanawa masu sha’awar zuwa wannan kasa yadda rayuwa take da irin abubuwan da ya kamata su yi idan suna sha’awar zuwa Amurka tare da zama cikinta.

1500-1530: Rahotannin Bayan Labaru

1500-1530: Kimiyya da Fasaha

Wannan shirin yana nazari da bayanin irin ci gaban da ake samu a kullu yaumin a fannonin kimiyya da fasaha a fadin duniya. A bayan fasahar kere-keren na’urorin zamani, da magunguna ana kuma duba ci gaba a binciken sararin samaniya.

1500-1530: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

2030-2100: Rahotannin Bayan Labaru, Rahotanni kan Harkokin Tattalin Arziki, Ra'ayin Gwamnatin Amurka

LARABA

0500-0530: Rahotannin Bayan Labaru

0500-0530: Sharhin Jaridun Amurka


Wannan shirin yana dubawa ya ga irin batutuwan da suka dauke wa jaridun Amurka hankali cikin wannan mako.

1500-1530: Rahotannin Bayan Labaru

1500-1530: Mu Kewaya Duniya Mu Sha Labari


Bayani dalla-dalla na batu mafi muhimmanci da ya fi dauke hankalin duniya ko akasarinta cikin wannan mako, da cikakken sharhi kan wannan batu.

1500-1530: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

2030-2100: Rahotannin Bayan Labaru, Rahotanni kan Ayyukan Alkinta Muhalli, Ra'ayin Gwamnatin Amurka

ALHAMIS

0500-0530: Rahotannin Bayan Labaru

0500-0530: Domin Iyali


Wannan fili yana tattauna batutuwan ad suka shafi iyali baki daya, musamman tarbiyyar yara, hakkin mata da yara da tattalin arzikinsu.

1500-1530: Rahotannin Bayan Labaru

1500-1530: Ra'ayoyin Masu Sauraro


A cikin wannan fili, masu sauraro suna iya bayyana ra’ayoyinsu, ko shawarwari, a game da shirye-shiryen Sashen Hausa na Muruar Amurka. A bayan wannan, mai sauraro yana iya aikowa da ra’ayinsa kan harkokin siyasar kasarsu, ko wani batu dake shafar al’ummar duniya, ko yin sharhi mai ma’ana ba na zagi ko cin zarafin wani ba.

1500-1530: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

2030-2100: Rahotannin Bayan Labaru, Rahotanni Kan Hanyoyin Sulhunta Rikice-Rikice, Ra'ayin Gwamnatin Amurka

JUMMA'A

0500-0530: Rahotannin Bayan Labaru

0500-0530: Lafiya Uwar Jiki


Wannan fili ya kan gayyato masana su tattauna batun kiwon lafiya, ko gabatar ad rahotanni a kan harkokin kiwon lafiya. Sannan kuma, likita yana shigowa ya amsa tambayoyin da masu sauraro suka yi dangane da lafiya.

1500-1530: Rahotannin Bayan Labaru

1500-1530: Addini A Amurka

Labarin yadda masu addinai dabam-dabam suke zaman tare, da yin cudanya da juna a Amurka, da irin batutuwan da suke fuskanta.

1500-1530: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

2030-2100: Rahotannin Bayan Labaru

2030-2100: Sai Bango Ya Tsage


Wannan fili ne dake gayyato shugabanni da manyan jami’ai dake bias wani mukami domin su amsa tambayoyin jama’a talakawa kan irin amanar da aka damka musu. A wasu lokuta kuma, a kan hada kwararru domin su fasa bakin wani batu mai muhimmanci ga masu sauraro.

2030-2100: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

ASABAR

0500-0530: Filin A Bari Ya Huce...

Hausawa suka ce, “a bari ya huce, shi yake kawo rabon wani.” Wannan fili nme dake kawo labarai na ban mamaki, ko ban dariya, ko ban haushi, ko na shirme! Ana kuma gaurayawa tare ad wakoki daga kowane lungu na duniya, tare da mika gaishe-gaishe ga wadanda suka rubuto wasiku zuwa ga wannan gidan rediyo.

0500-0530: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

1500-1530: Labarin Wasanni

Labarai da dumi-duminsu na wasannin motsa daga kowace kusurwa ta duniya, tare da mayar ad hankali musamman ga irin kokarin da kasashen Afirka suke yi a fannin wasanni a duniya.

1500-1530: Ra'ayin Gwamnatin Amurka

1800-1830: Karamin Sani, Kukumi


Wannan shiri yana gabatar da rahotanni na musamman kan yaki da cututtuka masu addabar matasa, kamar Kanjamau ko AIDS ko kuam SIDA, tarin fuka da sauransu. Haka kuma filin yana tabo sauran batutuwan da suke addabar matasa a wannan zamani. Sannan kuma, akwai jerin wakoki guda goma da suka fi farin jini a Amurka cikin wannan makon. Abin dai babu kama hannun yaro...