VOANews.com

Muryar Amurka ▪ Hausa Majiya Kwakkwara

16 Janairu 2009 

Yau A VOA:

Labarai Cikin Harsuna 45
  Ma'aikatan Sashen Hausa Na Muryar Amurka
Sunday DareSunday Dare

Sunday Dare shine shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, kuma tun kafin zuwansa nan Muryar Amurka a shekarar 2001, sanannen dan jarida ne a ciki da wajen Nijeriya. A shekarar 1998 Mr. Dare ya samu gurbin karo ilmin aikin jarida a Jami'ar New York, ya kuma sake samun irin wannan gurbi zuwa Jami'ar Harvard dake Cambridge a Jihar Massachussetts a shekarar 2000. Babban aikin da ya sanya a gaba yanzu shine kokarin tabbatar da cewa an biya wa masu sauraronmu bukatunsu na kawo labarai masu mihinmaci da la a kari, kuma da gaskiya ko wace rana.
Julie GreshamJulie Gresham 

Julie ta fara aiki da Muryar Amurka tun farkon shekarun 1990. A shekarar 1992 aka nada ta mai hada shirye shirye (wato Fardusa) ta sashen Portuguese, a 1997 kuma, lokacin da Fardusan Sashen Hausa Gloria Shorts tayi ritaya, sai aka hada mata shirye shiryen safe na Hausa da Portuguese gaba daya. Julie tayi aiki da Sashen Portuguese har na tsawon shekaru goma sha hudu, daga baya kuma ta amince ta dawo Sashen hausa, na maye gurbin Donnie Butler wacce tayi ritaya a shekarar 2006.

Ibrahim Alfa Ahmed 

Ibrahim Alfa Ahmed
 
Ibrahim Alfa Ahmed  "Mai Kahon Karo" shine editanmu na duniyar gizo. A bayan wannan ma, yana shiryawa tare da gabatar da filin nan na "A Bari Ya Huce..." da kuma shirin "Karamin Sani, Kukumi Ne" a kowane mako. Kafin ya taho nan Sashen Hausa a shekarar 1991, Ibrahim yayi aiki a NTA Bauchi. Kuma shi masoyin na'urori ne masu kwakwalwa, da wasanni, da kuma wake-wake da kade-kaden gargajiya da na zamani.

Jummai Ali Maduguri

Jummai Ali Maiduguri

Jummai Ali Maiduguri  Edita ce, kuma ita ce ke gabatar da shirin nan na "Lafiya Uwar Jiki" inda ake amsa tambayoyin masu sauraro game da batutuwan da suka shafi lafiya. Jummai ta fara aiki a Muryar Amurka tun shekarar 1984. Kafin nan kuwa, Jummai ta yi shekaru da dama tana aikin jarida a Kaduna.

Aliyu Mustapha SokotoAliyu Mustapha Sokoto

Aliyu Mustapha Sokoto,  "Gadanga Dokin Karfe" shi ma edita ne, kuma shine jagoran shirye-shiryen nan na "Amsoshin Tambayoyinku" da "Labarin Wasanni" wadanda kuke ji a ranakun asabar da lahadi. Aliyu yayi aiki a NTA Sokoto kafin ya taho nan Muryar Amurka a shekarar 1989. Aliyu ya jagoranci kungiyar nan ta "Zumunta" ta 'yan arewacin Nijeriya dake Amurka na tsawon shekaru da yawa dag kafa ta. A kwanakin baya kuma Allah Ya ba shi karuwa ta magaji, wanda aka radawa suna Usman. Allah Ya raya shi, amin.
Alhaji Kabiru FaggeAlhaji Kabiru Fagge

Alhaji Kabiru Fagge ya taho sashen Hausa na Muryar Amurka daga gidan telebijin na NTA Kano. Kafin nan kuwa yayi aiki a kamfanin buga jaridun New Nigerian da kuma hukumar alhazai ta Nijeriya. Alhaji Kabiru Fagge edita ne a Sashen Hausa, kuma shine ke jagorancin shirin "Ilmi Garkuwar Dan Adam" da "Sharhin Jaridun Amurka" a ko wane mako.
Grace Abdul AlheriGrace Abdu

Grace Alheri Abdu ita ce ke gabatar da shirin Domin Iyali. Kafin ta kama aiki a Muryar Amurka mataimakiyar darekta ce a gidan Rediyo da talabijin na jihar Plato (PRTVC).Tana da digiri a tauhidi da babban digiri a fannonin doka da diplomasiya; nazarin addinan gargajiya na nahiyar Africa da kuma babban diploma a fannin aikin jarida.
Umar Saa'd TudunwadaUmar Saa'd Tudunwada

Umar Saidu Tudunwada ya taho muryar Amurka daga gidan rediyon Freedom a kano, inda ya rike mukamin Mataimakin Janar Manaja. A baya kuma yayi aiki a Gidajen Talbijin na CTV da NTA, ya kuma dan taba aiki a Gidan Gwamnatin Jihar Kano, inda yayi aiki a matsayin Mataimakin Daraktan Yada Labarai, daga baya kuma Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman a Kan Hulda da Kafofin Yada Labarai. Umar, mai shekaru 46, Mutumin Tudunwadar Dankadai ne a Jihar Kano, kuma a Kanon yayi ilminsa tun daga Sakandire har zuwa Jami'a.
Halima Djimrao-KaneHalima Djimrao-Kane

Halima Djimrao-Kane ta taho Sashen Hausa na Muryar Amurka daga gidan rediyon Anfani a Yamai, Jamhuriyar Nijar. Ita ce ke gabatar da shirye-shiryen "Noma Tushen Arziki" da "Hira da Baki", sannan tana tallafawa "mai Kahon karo" wajen gabatar da filin A Bari Ya Huce....Halima 'yar Jamhuriyar nijar ce, koda yake tayi karatun turancin Ingilishi a Jami'ar Obafemi Awolowo dake Ife a Nijeriya.
Mohammed Danjuma UsmanMohammed Danjuma Usman

Mohammed Danjuma Usman ya kama aiki da Muryar Amirka tun shekara ta 1994 a matsayin mai aiki lokaci-lokaci. Ya fara aikin Rediyo tun daga gidan Rediyon Adamawa.

A yanzu yana tare da Sashen Hausa yana rike da shirin Gani ya kori Ji, da kuma aiki duniyar gizo gizo. Usman yayi digirinsa na farko a shirin fina-finai da aikin Rediyo a Kolejin Columbia a birnin Hollywood.

Sahabo Imam Aliyu

Sahabo Imam Aliyu

Sahabo Imam Aliyu ya zo sashen Hausa daga Jihar California ta Amurka inda yazo karatu a shekarar 1988.Yayi karatun digiri na farko a aikin Jarida a Kolejin Colubia dake Los Angeles,daga 1988-'92,sannan ya shiga Jami'ar La Verne dake birnin La verne a jihar California inda yayi digiri na biyu a aikin Jarida.Kamin zuwansa Amurka yayi aiki da gidan Radiyon Jihar Gongola (GBC Yola)kamin a raba jihar ta gida biyu.