VOANews.com

Muryar Amurka ▪ Hausa Majiya Kwakkwara

11 Janairu 2009 

Yau A VOA:

Labarai Cikin Harsuna 45
Isra'ila Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Cibiyoyin Hamas A Rana Ta 16 A Jere

11/01/2009

A mobile artillery piece fires towards targets in the southern Gaza Strip, on the Israel side of the border with Gaza, 10 Jan 2009
Bindigar igwa ta Isra'ila tana harbi cikin Gaza ranar asabar.
A rana ta 16 a jere, sojojin bani Isra'ila sun kai hare-hare a kan askarawan Hamas, suka kashe Falasdinawa su akalla 20 lahadin nan a fadin Zirin Gaza, duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke yi na a tsagaita wuta.

Shaidu sun ce tankoki da jiragen saman yaki na Isra'ila sun yi luguden wuta a kan sassan bayangarin birnin Gaza, yayin da askarawan Hamas suka harba makamai masu linzami na tarwatsa tankoki a kan sojojin bani Isra'ila dake kusantarsu.

Jami'an kiwon lafiya a yankin na Falasdinawa suka ce da yawa daga cikin wadanda aka kashe fararen hula ne. Isra'ila ta ce ba ta auna fararen hula, ta kuma zargi 'yan bindiga na Hamas da laifin cilla rokoki daga unguwannin fararen hula.

Ya zuwa yanzu, an kashe 'yan Isra'ila su 13, wadanda suka hada da sojoji 10 da fararen hula 3 da rokokin Falasdinawa suka kashe.

Jami'an kiwon lafiya na Gaza sun ce  an kashe Falasdinawa kimanin 850 a hare-haren da Isra'ila take kaiwa tun daga ranar 27 ga watan Disamba. Jami'ai sun kiyasta cewa rabin wadannan Falasdinawan da aka kashe fararen hula ne.


E-mail This Article Aika Labarin Nan ma Wani Ta E-Mail
Print This Article Shafi Mai Saukin Bugawa
  Muhimmin Labari

  Karin Labarai