|
Sojojin Isra'ila su na dauke wani dan'uwansu da ya ji rauni a fada
|
Sojojin kasa na
Isra’ila tare da tallafin jiragen helkwafta na kai farmaki sun kutsa can cikin
zirin Gaza, suka raba yankin na Falasdinawa dake bakin teku gida biyu.Ma’aikatan jinya a asibiti sun ce an kashe Falasdinawa su fiye da talatin,
akasarinsu fararen hula, yau lahadi a yayin da sojojin bani Isra’ila da na
Hamas suke ba-ta-kashi a kan tituna. Rundunar sojojin bani Isra’ila ta ce an ji
rauni ma sojojinta 30.
Wani kakakin firayim minista Ehud Olmert na Isra’ila ya
fada ma gidan telebijin na al-Jazeera cewa Isra’ila zata ci gaba da wannan
farmakin har sai an samu hanyar cimma zaman lafiya mai dorewa.
Cikin daren asabar Isra’ila ta umurci sojojinta na kasa da su kutsa cikin Gaza a bayan da ta shafe
mako guda tana kai farmaki ta sama a kan yankin. Jami’an sojan Isra’ila suka ce
ba aniyarsu ce su sake mamaye Gaza ba, su na so ne su lalata dukkan cibiyoyin
Hamas a wannan yanki.
‘Yan kishin Hamas sun cilla rokoki kimanin 25 daga
maraicen asabar zuwa safiyar lahadi a kan kudancin Isra’ila. Roka guda ta fada
kan wani gini a birnin Ashdod ta ji rauni wa mutane biyu.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Ban Ki-moon, yayi kira ga Isra’ila da ta ja burki ma wannan farmaki nata na
sojojin kasa. Amma kuma Kwamitin Sulhun MDD ya kammala taron gaggawa da ya fara
da maraicen asabar ba tare da cimma daidaituwa kan lamarin ba. Jami’an
diflomasiyya suka ce Amurka ta sa kafa ta toshe hanyar amincewa da wani kudurin
da kasar Libya ta gabatar dake kiran da a kawo karshen wannan fada nan take.
Jami’ai sun ce an kashe Falasdinawa akalla 500 tun lokacin da Isra’ila ta fara
kai hare-hare.